Isa ga babban shafi
TARON-ECOWAS

Shugabannin ECOWAS na taron gaggawa akan juyin mulkin Guinea

Shugabannin kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS na gudanar da wani taron gaggawa a kasar Ghana dangane da juyin mulkin da sojoji suka yi a Guinea wanda ya kawar da zababben shugaban kasa Alpha Conde daga karagar mulki.

Shugabannin ECOWAS a Ghana
Shugabannin ECOWAS a Ghana © Nigeria presidency
Talla

Tuni shugabannin kungiyar suka dakatar da kasar Guinea daga cikin su da kuma tura tawaga wadda taje Conakry ta kuma gana da shugabannin sojojin a karkashin jagorancin Kanar Mamady Doumbouya da kuma hambararen shugaban kasar Conde.

Shugabannin ECOWAS yayin bude taron su a Accra
Shugabannin ECOWAS yayin bude taron su a Accra © Nigeria presidency

Yayin bude taron shugaban kungiyar ECOWAS kuma shugaban Ghana Nana Akufo-Addo yace ana bukatar su da su yanke hukunci bayan sauraron ba’asi daga tawagar wakilan da suka ziyarci Guinea, yayin da ya bukaci goyan bayan sauran shugabannin kasashen yankin 15 dake halartar taron.

Ministar harkokin wajen Ghana Shirley Ayorkor Botchwey wadda ta jagoranci tawagar da ta je Guinea tace shugababbin sojin na da hurumin gabatar da shirin mayar da mulki ga fararen hula, amma kungiyar ECOWAS ce zata yanke hukunci akai.

Shugaban ECOWAS Nana Akuffo-Ado tare da takwarorin sa da kuma tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Shugaban ECOWAS Nana Akuffo-Ado tare da takwarorin sa da kuma tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan © Nigeria presidency

Ana kuma sa ran taron ya saurari bayanai daga tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan wanda ke shiga tsakani wajen ganin sojojin da suka yi juyin mulki a Mali sun cika alkawarin da suka dauka na gudanar da zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.