Tsohon shugaban Guinea na cikin koshin lafiya - ECOWAS
Wakilan kungiyar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS sun ce, hambararren shugaban kasar Guinea Alpha Conde na cikin koshin lafiya.
Wallafawa ranar:
Wakilan tawagar ta ECOWAS sun bada tabbacin ne yayin ziyarar da suka fara a kasar jiya Juma’a don ganawa da sojojin da suka yi juyin mulki a karkashin Lafatanar Kanal Mamady Dambouya.
A makon da ya kare ne dai kungiyar kasashen na yammacin Afirka ta dakatar da Guinea daga cikinta, yayin da kuma a Juma’ar nan, kungiyar kasashen Afirka AU ta bi sahu.
Shugaban Hukumar Gudanarwar ECOWAS Jean-Claude Kassi Brou, wanda ke cikin tawagar da ta sauka a birnin Conakry, ya ce masu shiga tsakani sun gana da tsohon shugaba Conde kuma yana samun kulawa mai kyau.
Juyin mulkin da aka yi a Guinea dai shi ne na 4 cikin watanni 13 a Yammaci da kuma Tsakiyar Afirka, abin da ya tayar da hankalin masu sa ido kan yadda gwamnatocin da sojoji ke jagoranta ke karuwa a yankunan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu