Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

An kashe mutane fiye da 120 a yankin Amhara na Habasha

Likitoci da jami’an Amhara sun ce an kashe fararen hula sama da 120 a yankin da ke kasar Habasha a farkon wannan watan.

Wasu daga cikin mayakan sa kai a yankin Amhara da ke arewacin kasar Habasha.
Wasu daga cikin mayakan sa kai a yankin Amhara da ke arewacin kasar Habasha. EDUARDO SOTERAS AFP
Talla

Kashe-kashen a kauyen Chenna, da ke kusa da garin Dabat, ya faru ne a farkon watan Satumba, a cewar Sewnet Wubalem, mai kula da yankin na Dabat, da kuma Chalachew Dagnew, mai magana da yawun birnin Gonar da ke kusa da inda lamarin ya auku.

Sai dai cikin sanawar da suka fitar ‘yan tawayen Tigray sun yi watsi da abin da suka kira labarain da da gwamnatin yankin Amhara ta kirkira.

‘Yan tawayen na Tigray sun kuma musanta a hannu a kisan fararen hular fiye da 100.

Tun daga watan Nuwamban shekarar 2020, arewacin kasar Habasha ke fama da rikice-rikice, lokacin da Fira Minista Abiy Ahmed ya tura sojoji zuwa Tigray don kawar da jam'iyya mai mulkin yankin ta TPLF, matakin da ya ce martani ga hare-haren da mayakan ‘yan tawayen TPLF ke kaiwa sansanin sojoji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.