Isa ga babban shafi
Tigray

Sojojin Habasha sunyi ikirarin kasashen 'yan tawaye sama da dubu 5

Rundanar Sojin Habasha tayi ikrarin kashe Yan tawayen TPLF dake Yankin Tigray sama da dubu 5 a fafatawar da suke ci gaba da yi a yankin arewacin kasar.

'Yan tawayen yankin Tigray na kasar Habasha
'Yan tawayen yankin Tigray na kasar Habasha Yasuyoshi Chiba AFP/File
Talla

Shugaban sojin Laftanar Janar Bacha Debele ya sanar da adadin mutane sama da 5,600 da dakarun kasar suka hallaka ba tare da karin bayani akan lokacin da aka kashe su ba.

Janar Debele da ya zargi ‘Yan Tawayen TPLF da kokarin raba kasar ya kuma ce an jikkata sama da 2,300 daga cikin su, yayin da aka kama sama da 2,000 a matsayin firsinan yaki.

Tashin hankali ya barke tsakanin ‘Yan Tawayen da dakarun gwamnati a watan Nuwambar bara, lokacin da Firaminista Abiy Ahmad ya tura tawagar soji domin murkushe tawayen shugabannin Yankin Tigray.

Rahotanni sun ce rikicin yayi sanadiyar mutuwar dubban mutane, yayin da wasu kuma suka gudu zuwa Sudan domin samun mafaka.

Majalisar dinkin duniya da kungiyoyin agaji sun zargi bangarorin biyu da aikata laifuffukan yaki da suka hada da kashe fararen hula da kuma yiwa mata fyade, yayin da ake fargabar samun fari a yankin saboda dakile motocin dake safarar kayan abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.