Isa ga babban shafi
Tigray

MDD da AU sunyi kira ga Habasha kan barin kayan agaji isa yankin Tigray

Kungiyar Tarayyar Afirka ta bukaci gwamnatin Habasha da ta kara kaimi wajen tabbatar da isar da kayan agaji ga yankin Tigray da yaki ya daidaita don hana bala’in yunwa, yayin da ma'aikatan agaji ke kokarin kaiwa ga mutanen da ke cikin mawuyacin hali.

Wasu 'yan yankin Tigray na kasar Habasha dake jiran kayan agaji.
Wasu 'yan yankin Tigray na kasar Habasha dake jiran kayan agaji. REUTERS - BAZ RATNER
Talla

Arewacin Habasha na fama da tashe -tashen hankula tun daga watan Nuwamba, lokacin da Firanminista Abiy Ahmed ya tura sojoji zuwa Tigray don murkushe kungiyar 'yan tawayen Tigray (TPLF), dake mulkin yankin, yana mai cewa matakin ya zo ne a matsayin martani ga hare -haren da aka kai kan sansanin sojoji.

Itama Majalisar Dinkin Duniya tace yanzu haka miliyoyin 'yan kasar Habasha da ke zaune a arewacin kasar na cikin barazana da kunchi, saboda hana shigar da kayan agaji yankin.

A wani mataki da ke zaman gargadi, Majalisar ta ce hakan na tattare da matsaloli da masu yawan gaske.

Yaƙin da aka shafe shekaru goma ana gwabazawa tsakanin dakarun gwamnati da ‘yan tawayen Tigray, ya jefa mutane da dama cikin halin ni’iyasu da kuma bukatun agaji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.