Isa ga babban shafi
AFIRKA TA TSAKIYA

Wani kamfanin Faransa ya kulla yarjejeniyar sirri da 'yan tawaye - The Sentry

Wata kungiyar Amurka ta zargi reshen rukunin kamfanin Castel na Faransa dake jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da ya kulla yarjejeniyar sirri da ‘yan tawayen kasar dake dauke da makamai wajen kere mata masana’antu shi kuma yana biyan su kudade da sauran bukatu tsawon shekaru da dama, zargin da kamfanin ya musanta.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadéra  yayin wata ganawa da Faransa 5/09/19
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadéra yayin wata ganawa da Faransa 5/09/19 AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

A cikin rahotan da ta fitar wannan Laraba kungiyar mai zaman kanta mai suna The Sentry ta zargi reshen kamfanin Castel na Faransa Sucaf dake samar da sukari a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

A cewar kungiyar mai zaman kanta ta Amurka, wacce ta kware wajen bin diddigin mu’amalar kudaden haramun, tace kamfanin ya “tattauna da kungiyar ‘yan tawayen UPC daya daga cikin kungiyoyin tawaye masu dauke da makamai a Afirka ta Tsakiya da ake zargi da cin zarafin bil’adama.

The Sentry tace, kamfanin ya dauki tsawon lokaci yana baiwa mambobin kungiyar mai dauke da makamai makudan kudade kai tsaye da kuma wasu hanyoyi ta daban, sai kuma gyaran ababen hawansu da kuma samar musu da man fetir, yayin da kungiyar ke samar da tsaron kamfanin da gonaken sa na rake dake yankin.

Tuni kamfanin ya musanta zargin ta bakin shugaban reshen Somdiaa, Alexandre Vilgrain, wanda ya shaidawa kamfanin dillancin larai na AFP cewa bubu wani makaicin tallafi da suka baiwa kungiyar ta ‘yan tawaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.