Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya-Faransa

CAR ta gurfanar da Bafaranshen da ta zarga da yi mata leke

Masu gabatar da kara a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya sun gurfanar da wani Bafaranshe bisa zargin sa da leken asiri da cin amanar kasa, matakin da ya fusata kasar Faransa, wadda ita kuma ta zargi Afrika ta Tsakiyar da yin amfani da farfagandar Rasha.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da takwaransa na Tsakiyar Afrika Faustin-Archange Touadéra,
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da takwaransa na Tsakiyar Afrika Faustin-Archange Touadéra, AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

Juan Remy Quignolot shi ne Bafaranshen da jami’an tsaron Jamhuriyar Afrika ta Tsakiyar suka kame a birnin Bangui a ranar 10 ga watan Mayun da ya gabata, tun lokacin kuma yake tsare, inda yake jiran fuskantar tuhume-tuhume kan laifukan leken asiri da mallakar makaman soji da na farauta ba bisa ka’ida ba, da kuma shirya makarkashiyar cin amanar kasar ta Afrika ta Tsakiya ta hanyar hadin baki da miyagu.

Yayin sanar da jerin tuhume-tuhumen da ake yi wa Bafaranshen, babban mai gabatar da karar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Eric Didier Tambo ya ce, za a soma shari’ar nan da watanni 6, sai dai bai bayyana hukuma ko kasar da mai laifin ke yi wa aiki ba.

Matakin Afrika ta Tsakiyar na zuwa ne kwanaki 2 bayan da Faransa ta dakatar da aikin hadin gwiwa na soji tsakaninta da kasar da ta taba yi wa mulkin mallaka bisa zargin ta da hada kai da Rasha wajen yi mata zagon kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.