Isa ga babban shafi

Macron ya yi Allah wadai da 'yan tawaye a Afrika ta Tsakiya

Fadar gwamnatin Faransa ta Elysee ta ce, shugaban kasar Emmanuel Macron ya tattauna da takwaransa na jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Faustin Archange Touadéra, inda ya sake jaddda rashin goyon bayan sa kan yunkurin da gungun 'yan tawaye tare da wasu shuwagabanin 'yan siyasa, ciki har da tsohon shugaban kasar François Bozizé, ke yi wajen haifar da tarnaki ga zabukan kasar.

'Yan tawaye a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya
'Yan tawaye a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya AFP/ALEXIS HUGUET
Talla

Tattaunawar na zuwa ne kwanaki hudu bayan sake zaben shugaba Touadéra  da kuma sanarwa da mai shigar da karar Bangui ya fitar ta soma bincike Mista Bozizé kan alaka da 'yan tawaye.

Bisa bukatar shugaba Touadéra ne shugaban na Faransa Emmanuel Macron ya umarci dakarun Faransa suka gudanar da sintirin tsaron jiragen saman yaki a fadin jamhuriyar Afrika ta Tsakkiya a ranar juma’ar da ta gabata, bayan suntirin farko da ya gabata a ranar 23 ga watan Disambar bara, domin nuna kyakywan goyon bayan Faransa ga al’ummar kasar, tare da yin tir da Allah waddai da yinkurin rikitar da kasar da kungiyoyin dake dauke da makamai ke shirin yi, in ji sanarwar ta sanar.

Yan takarar jam'iyyun adawa 10 ne dai, suka bukaci soke zaben shugabancin kasar da na 'yan majalisar dokokin da aka gudanar a ranar 27 ga watan Disamba da ya gabata, zaben da suka ce mutum guda ne cikin 2 ne kadai suka halarce shi.

Makwanni 3 ne da suka gabata 'yan tawaye suka yi barazanar hana gudanar da zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisa a kasar dake fama da  yakin basasa da ta yi fama da shi tun cikin 2013 zuwa 2018 na bara.

fadar shugaban kasar ta Faransa ta ce Shugaban Macron ya bukaci bangarorin siyasar kasar da mutunta hukuncin da kotun fasalta kundin tsarin mulkin kasar, duk da haka ya kuma yi kiran bude tattaunawar siyasa da zai hada kowa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.