Isa ga babban shafi
Faransa-Afrika ta Tsakiya

Faransa ta daina bai wa CAR agaji saboda karya

Faransa ta dakatar da bai wa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya agaji saboda zargin gwamnatin kasar da hannu wajen yada labaran karya dangane da kasar wanda ke samun goyan bayan kasar Rasha.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron AP - Christophe Ena
Talla

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa ya rawaito Ma’aikatar Tsaron Faransa na cewar a karo da dama hukumomin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun dauki alkawuran da suka kasa cikawa, musamman abin da ya shafi siyasa da 'yan adawa da kuma alaka da ita kan ta Faransa da ake bata suna.

Yayin da ake kallon Rasha a matsayin wadda ke kitsa batawa Faransa baya, hukumomin kasar na dangata matsalar da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wadda ta bada damar yin haka.

Tuni wasu sojojin Faransa 5 da ke bai wa hukumomin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar shawara suka koma gida bayan katse horon da suke bai wa takwarorinsu na kasar.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Faransa ta ki yin cikakken bayani kan adadin agajin da Faransa ke bai wa kasar kowacce shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.