Isa ga babban shafi

Sabon jakadan Faransa ya kama aiki a Rwanda

Tun daga lokacin da shugaba Emmanuel Macron ya kai ziyara Rwanda daga ranar 27 ga watan mayun wannan shekara har ma ya gana da shugaban kasar Paul Kagame, ana iya cewa an samu kyautatuwar alaka tsakanin kasashen biyu, inda a jiya alhamis sabon jakadan Faransa ya fara aiki a birnin Kigali na kasar ta Rwanda.

Shugaban Faransa ,lokacin da ya ziyarci kasar Rwanda
Shugaban Faransa ,lokacin da ya ziyarci kasar Rwanda AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

Bayan ganawarsa da shugaba Kagame, sabon jakadan Faransa a Rwanda Antoine Anfré ya shaida wa Christophe Karenzi na sashen Kiswaili na rfi cewa,bayan rahoton bincike na Duclert da kuma ziyarar da shugaba Macron ya kai, ana iya cewa an bude sabon babi na alaka tsakanin Faransa da Rwanda.

Shugaban Faransa  eMMANUEL macron lokacin da ya ziyarci kasar Rwanda
Shugaban Faransa eMMANUEL macron lokacin da ya ziyarci kasar Rwanda REUTERS - JEAN BIZIMANA
Tabbas Faransa na da manyan manufofi abin da ke nufin cewa akwai gagarumin aiki a gaban kasar ta Faransa. Antoine Anfré ya tabbatar da cewa suna da kyakkyawar manufa, lura da abubuwan da suka faru lokacin ziyarar Shugaba da Macron ya kawo har ma ya kaddamar da cibiyar raya al’adu a birnin Kigali.

Har ila yau akwai hukumar AFD da ke gudanar da ayyukan raya kasa da za ta bude ofishinta a birnin Kigala kafin karshen wanan shekara.

Akwai kamfanoni da masana’antun Faransa da ke wannan kasa, kamar ‘’Bollore’’ Antoine Anfré y ace ya na da yakinin cewa za a samu sakamakon mai kyau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.