Isa ga babban shafi
Rwanda-Faransa

Macron zai ziyarci Rwanda don gyara alakar kasar da Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai ziyarci kasar Rwanda domin inganta dangantaka tsakanin kasashen biyu bayan matsalar da aka samu a tsakanin su.

Shugaba Emmanuel Macron tare da takwaransa na Rwanda Paul Kagame yayin taron tattalin arzikin Afrika da ya gudana a birnin Paris.
Shugaba Emmanuel Macron tare da takwaransa na Rwanda Paul Kagame yayin taron tattalin arzikin Afrika da ya gudana a birnin Paris. © RFI/Pierre René-Worms
Talla

Wannan ita ce za ta zama ziyara ta farko da wani shugaban Faransa zai kai kasar a cikin shekaru 11 tun bayan ziyarar da tsohon shugaban kasa Nicolas Sarkozy ya kai a watan Fabararirun shekarar 2010.

Ana saran shugaban ya gana da takwaran sa Paul Kagame da kuma bude ofishin jakadancin kasar.

Alaka na shirin dawowa tsakanin kasashen biyu ne bayanda Emmanuel Macron ya yi umarnin bibiyar bayanai kan kisan kiyashin Rwandan, bayanan da suka gano yadda Faransar ta zuba ido ba tare da daukar mataki lokacin faruwar lamarin ba, inda kasar ta nemi yafiyar Rwanda kan batun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.