Isa ga babban shafi
Faransa - Rwanda

Shugaban Rwanda ya jinjinawa Faransa kan rahoton kisan kiyashin 1994

Shugaban Rwanda, Paul Kagame ya ce rahoton binciken kisan kiyashin kasar na shekarar 1994 da masana tarihi suka fitar a watan Afrilun da ya gabata, abu ne da zai iya share fagen dawo da kyakkyawar alaka tsakanin Rwanda da Faransa.

Shugaban Rwanda Paul Kagame, yayin zantawa da RFI da kuma France24. 17/5/2021.
Shugaban Rwanda Paul Kagame, yayin zantawa da RFI da kuma France24. 17/5/2021. © RFI
Talla

Shugaba Kagame ya jinjinawa kokarin na Faransa ne a yayin ziyarar aiki da yake yi a kasar.

A zantawarsa da tashar talabijin ta France24 da kuma RFI, shugaba Kagame, yayi tsokaci kan rahoton binciken dake cewa Faransa da na alhaki a kisan kiyashin wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dubu 800 mafi yawansu ‘yan kabilar Tutsi.

Fitaccen masanin tarihii kuma babban jami'in gwamnatin Faransa Vincent Duclert a birnin Kigali, yayin mikawa shugaban Rwanda Paul  Kagame rahoto kan kisan kiyashin da aka yiwa mutane fiye da dubu 800, mafi akasari 'yan kabilar Tutsi a 1994. 9/4/2021.
Fitaccen masanin tarihii kuma babban jami'in gwamnatin Faransa Vincent Duclert a birnin Kigali, yayin mikawa shugaban Rwanda Paul Kagame rahoto kan kisan kiyashin da aka yiwa mutane fiye da dubu 800, mafi akasari 'yan kabilar Tutsi a 1994. 9/4/2021. AFP - SIMON WOHLFAHRT

A lokacin da aka tambayi Kagame kan ko zai nemi Faransa ta nemi afuwa kan rawar da ta taka wajen kisan kiyashin da aka yi na shekarar 1994, sai shugaban na Rwanda ya ce zai yi matukar farinciki idan har gwamnatin Faransar za ta nemi afuwar.

Shugaban ya kuma tattauna kan hare-haren ‘yan bindigar da makwafciyarsa Jamhuriyar Congo ke fama da su yayin zantawarsa da RFI da kuma France24.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.