Isa ga babban shafi
Faransa - G5 Sahel

Kasashen G5 da Faransa na taro kan tsaron yankin Sahel

A wannan Juma'a ake ganawa tsakanin shugabannin kasashen G5 na yankin Sahel da kuma Faransa kan makomar yaki da ayyukan ta’addancin da suka addabin yankin, wadanda ke cigaba da salwantar da rayukan jama’a da kuma dukiya.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin wata ganawa da shugabannin kasashen yankin Sahel ta kafar bidiyo
Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin wata ganawa da shugabannin kasashen yankin Sahel ta kafar bidiyo Francois Mori POOL/AFP
Talla

Bayan share sama da shekaru 8 da girke sojojinta a Sahel, a karshen watan Yunin 2021 shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana kawo karshen rundunar sojin Barkhane, tare da rage yawan sojojin kasar su dubu 5 da 100 zuwa kasa da dubu 1, da kuma sanar da yankurin kafa wata sabuwar rundunar yaki da ‘yan ta'adda mai suna Takuba ta kasashen duniya da za su hada da na nahiyar Turai.

Tattaunawar da shugaban  Faransa zai yi  ta hoton bidiyo  da takwarorinsa na kasashen G5 Sahel, da suka hada da na Mauritania, Chadi, Mali, Burkina Faso, da Jamhuriyar Nijar za ta maida hankali ne kan sabunta tsarin yaki da ta’addanci da kuma batun kafuwar sabuwar rundunar Takuba, wadda za ta maye ta Barkhane.

A matakin farko Faransa za ta fara janye sojojinta kimanin  dubu 3 da 500 ne nan da shekara guda, kana wasu dubu 2 da 500 su biyo baya, nan da karshen shekarar  2023, kamar yadda wata majiya daga hukumomin tsaron kasar ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.