Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu - Yaki

Halin da Sudan ta Kudu ke ciki shekaru 10 bayan kafuwa a matsayin kasa

Sudan ta Kudu ta cika shekaru 10 da kafuwa a matsayin kasa, burin da ta cimma ta hanyar kada kuri’ar jin ra’ayin jama’a tare da ballewa daga tsohuwar kasar Sudan, bayan fadan da bangarorin biyu suka gwabza.

Dubban 'yan kasar Sudan ta Kudu yayin murnar ballewar kasar daga tsohuwar Sudan a watan Yulin shekarar 2011. Sai dai jim kadan bayan bikin yakin basasa ya barke a kasar.
Dubban 'yan kasar Sudan ta Kudu yayin murnar ballewar kasar daga tsohuwar Sudan a watan Yulin shekarar 2011. Sai dai jim kadan bayan bikin yakin basasa ya barke a kasar. Roberto SCHMIDT AFP/File
Talla

To sai dai mahukunta sun ce a bana ba wani bikin da za a gudanar don murnar zagayowar wannan rana, lura da halin matsin tattalin arziki, sai kuma yakin basasa da yunwa da suka shafi miliyoyin mutanen kasar.

A cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar mai arzikin man fetur ta fada cikin tashin hankalin yakin basasa wanda yayi sanadin kashe mutane kusan dubu 400, yayin da kuma a gefe guda matsalolin tagayyarar miliyoyin mutane saboda yunwa da karancin magunguna tare da cin hanci da rashawa suka addabi kasar.

Al’ummar Sudan ta Kudu dai sun kasance cike da kyakkyawan fata a shekarar 2011 lokacin da suka balle daga tsohuwar Sudan.

Bayan shafe shekaru da yawa suna gwabza yaki da bangaren arewacin tsohuwar kasar ta Sudan ne bangaren Kudu ya jefa kuri'a mafi rinjaye don ballewa, inda aka rantsar da Salva Kiir, tsohon madugun ‘yan tawaye, a matsayin shugaban Sudan ta Kudu na farko, tare da Riek Machar, a matsayin mataimakinsa.

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir tare da mataimakinsa Riek Machar a shekarar 2020.
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir tare da mataimakinsa Riek Machar a shekarar 2020. ALEX MCBRIDE AFP

Jim kadan bayan kafuwar sabuwar gwamnatin kasar Sudan ta Kudu rikici ya barke tsakanin shugaba Kiir da Machar, abinda ya sa a watan Yulin 2013, Kiir ya kori Machar da dukkanin majalisar ministocinsa, sannan mummunan yakin basasa ya barke watanni biyar bayan haka.

A waccan lokacin dai duk wani yunkuri na kawo karshen yakin basasar bai samu nasara ba, saboda gazawar yarjejeniyar raba madafun iko ta farko a 2015 tsakanin gwamnatin Kiir da madugun ‘yan tawaye kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Riek Machar.

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir tare da mataimakinsa kuma tsohon madugun 'yan tawaye Riek Machar a birnin Juba bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar sulhu da kuma kafa sabuwar gwamnatin hadin gwiwa a ranar 17 ga Disambar 2020.
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir tare da mataimakinsa kuma tsohon madugun 'yan tawaye Riek Machar a birnin Juba bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar sulhu da kuma kafa sabuwar gwamnatin hadin gwiwa a ranar 17 ga Disambar 2020. AFP/File

A shekarar 2018 ne kuma aka sake kulla yarjejeniyar zaman lafiya ta biyu inda bangarorin da ke fada da juna suka kafa gwamnatin hadin gwiwa a bara, inda a yanzu haka shugaba Kiir da Machar ke kokari karo na uku don tafiyar da mulkin kasar ta Sudan ta Kudu.

Sai dai a yayin da aka samu nasarar dakatar da yakin basasar kasar, har yanzu ana ci gaba da samun rikicin kabilanci da na kan iyaka tsakanin wasu kabilun kasar, zalika har yanzu ba a kai ga  aiwatar da wasu muhimman sassan yarjejeniyar kafa gwamnatin hadakar da aka kulla ba, musamman wajen gauraya sojojin kasar da na 'yan tawaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.