Isa ga babban shafi
GHANA-SUFURI

Akufo-Addo ya kaddamar da aikin gina hanyar Pokuase

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya kaddamar da wani gagarumin aikin gadar sama da zata saukakawa matuka ababan hawa a Pokuase, wanda aka bayyana cewar shine irin sa na farko a Yankin Afirka ta Yamma.

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo yana kaddamar da hanyar Pokuase
Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo yana kaddamar da hanyar Pokuase © Ghana Presidency
Talla

Yayin kaddamar da gadojin a wani biki da ya samu halartar daruruwan jama’a, shugaban yace gwamnatin sa ta dauki aniyar gudanar da aikin ne domin saukakawa matafiya da kuma rage haduran da ake samu.

Akufo-Addo yace da farko an bada kwangilar gina gadojin ne guda 3 amma daga bisani sai aka sake nazari inda aka kara yawan su zuwa guda 4 a karkashin kwangilar guda.

Hoton gadar saman Pokuase da shugaba Nana Akufo-Addo ya kaddamar
Hoton gadar saman Pokuase da shugaba Nana Akufo-Addo ya kaddamar © Ghana Presidency

Shugaban ya yabawa Bankin kasashen Afirka na AfDB wanda ya bada gudumawa wajen gudanar da aikin na hadin gwuiwa tare da gwamnatin Ghana.

Akufo-Addo ya kuma bukaci al’ummar kasar da zasu ci gajiyar hanyar, musamman direbobin mota, da su tabbatar da amfani da dokokin tuki wajen kare lafiyar jama’a.

Wani bangare na hanyar Pokuase
Wani bangare na hanyar Pokuase © Ghana Presidency

Shugaban yace shirin sake fasalin Ghana domin ganin tayi tafiya da zamani ya kankama, inda ya bukaci goyan bayan daukacin Yan kasar da su bashi goyan bayan domin cimma nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.