Isa ga babban shafi
Mozambique

'Yan ta'adda sun sace kananan yara 51 a Mozambique- Save the Children

Kungiyar Agaji ta Save the Children ta koka da bayanan da ke cewa ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi sun sace gomman yara, kanana galibi mata a cikin shekaru ukun baya bayan a Mozambique bayan tsanantar ayyukan ta’addanci a kasar ta Nahiyar Afrika.

Wasu da rikici ya raba da matsugunansu a yankin Cabo Delgado, na Mozambique.
Wasu da rikici ya raba da matsugunansu a yankin Cabo Delgado, na Mozambique. AFP - ALFREDO ZUNIGA
Talla

Kungiyar agajin ta Birtaniya, ta ce akalla kananan yara 51 ‘yan ta’addan suka sace a cikin kasar wadda karuwar ayyukan ta’addanci ya tilastawa dubunnan mutane rasa matsugunansu.

Kungiyar cikin sanarwar da ta fitar ta ce da yiwuwar alkaluman ya zarta wanda ta sanar la’akari da cewa iyakar wadanda ta samu labari ne kawai ta bayyana dai dai lokacin da mayakan ta’addanci ke zafafa hare-hare tare da sace sacen a sassan kasar.

Save the Children ta nuna matukar damuwa kan yadda kungiyoyin ta’addanci ke karkata ayyukan ta’addancinsu kan kananan yaran da basu ji ba basu gani ba, wanda ta bayyana da tsagwaron take hakkin yara a dokokin Duniya.

Daraktan kungiyar ta Save the Children, mai kula da Mozambique Chance Briggs ya ce matsalolin tsaro hare-haren ‘yan ta’addan na barazana ga samun nutsattiyar rayuwa mai kunshe da ingantaccen ilimi ga kananan yaran kasar har ma da matasa.

Cikin shekarun ukun baya-bayan ne hare-haren ta’addanci suka tsananta a arewacin kasar ta Mozambique musamman kan garuruwa da kauyukan bayan gari, wanda ya sanya mutane dubu 700 tsere kuma kusan rabin adadin kananan yara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.