Al'ummar Palma dubu 5 da rikici ya kora sun samu mafaka a cikin Mozambique
Majalisar Dinkin Duniya ta ce 'yan gudun hijira sama da 5,000 da suka gudu domin tsira da rayukan su daga rikicin da ake yi a garin Palma da ke kasar Mozambique yanzu haka sun samu mafaka.
Wallafawa ranar:
Mai magana da yawun hukumar kula da kaurar baki ta Majalisar Sandra Black ta ce ya zuwa ranar Talatar da ta gabata, sun kidaya mutane dubu 5 da 360 da suka isa yankunan Nangade da Mueda da Montepuez da kuma Pemba.
Rahotanni sun ce mutane da dama sun mutu sakamakon hare haren da 'yan tawayen yankin suka kai wadanda ke ikrarin jihadi.
Rikicin 'yan bindigar ya yi sanadiyar raba mutane kusan 670,000 daga muhallin su a yankin dake da arzikin iskar gas.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu