Guguwar Eloise ta rushe gidaje fiye da dubu 5 a Mozambique
Hukumomin agaji a Mozambique sun ce dubban mutane sun rasa muhallansu sakamakon guguwar Eloise da ta ratsa kasar a karshen mako.
Wallafawa ranar:
Rahotanni sun ce guguwar dake gudun kilomita 150 kowacce sa’a, dauke kuma da ruwan sama, ta afkawa birnin Beira dake gabar ruwa, abinda yayi sanadin raba mutane akalla dubu 7 da gidajensu, yayin da gidaje sama da dubu 5 suka rushe.
Hukumar again gaggawa tace mutane 6 sun mutu a hadarin, kana wasu 12 sun jikkata.
Shekaru biyu da suka gabata dai guguwar Idai ta tafka mummunar barna a garin na Beira dake gabar ruwa, inda ta salwantar da rayukan mutane da dama da kuma janyo hasarar dimbin dukiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu