Isa ga babban shafi
Mozambique-Ta'addanci

'Yan ta'adda na shirin sake kai farmaki a arewacin Mozambique - Kwararru

Wata cibiyar gudanar da bincike, hasashe gami da bada shawarwari kan lamurran da suka shafi tsaro, tattalin arziki da kuma siyasa mai suna Pangea-Risk, ta ce mayakan ‘yan ta’adda na shirye-shiryen sake afkawa wasu yankunan arewacin Mozambique mai fama da hare-haren ta’addanci.

Wani yanki dake kusa da Palma a arewacin kasar Mozambique, garin da ya fuskanci hare-haren 'yan ta'adda.
Wani yanki dake kusa da Palma a arewacin kasar Mozambique, garin da ya fuskanci hare-haren 'yan ta'adda. AP - Dave LePoidevin
Talla

Pangea-Risk dake da babban ofishnta a birnin London ta ce bayanan sirrin da ta samu sun nuna cewar ‘yan ta’addan za su kai sabon farmakin ne nan da ‘yan makwanni kan garin Quitanda dake kusa da filin hakar isakar gas na Afungi dake lardin Cabo Delgado.

Tun daga shekarar 2017, mayaka masu ikirarin Jihadi da suka yyiwa kungiyar IS mubaya’a suka kaddamar da hare-haren a arewacin kasar Mozambique, inda kawo yanzu suka kame wasu yankuna.

Wasu 'yan kasar Mozambique da hare-haren ta'addanci kan garin Palma ya tilasta musu yin gudun hijira.
Wasu 'yan kasar Mozambique da hare-haren ta'addanci kan garin Palma ya tilasta musu yin gudun hijira. AP

Kididdigar baya bayan nan dai ta nuna cewar mayakan da aka fi kira da Al-Shabaab, sun kashe dubban mutane, tare da tilastawa wasu akalla dubu 700 tserewa daga muhallansu, sakamakon hare-haren da suka kaddamar kan yankin arewacin Mozambique, musamman a lardin Cabo Delgado.

Yankin na Cabo Delgado da yayi iyaka da kasar Tanzania, na tattare da arzikin isakar gas mai yawan gaske.

Har yanzu dai shugaban Mozambique Filipe Nyusi ya ki amincewa da karbar taimakon sojoji daga kasashen ketare domin taimakawa kasar wajen murkushe barazanar ta’addancin da ke ci musu tuwo a kwarya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.