Namibia ta yi watsi da diyyar Jamus kan kisan kiyashin mulkin mallaka
Sarakunan gargajiyar Namibia sun yi watsi da neman afuwar da Jamus ta yi gami da alkawarin biyansu diyyar akalla euro biliyan 1, saboda kisan kiyashin da dakarunta suka yiwa dubban jama’a a kasar a zamanin mulkin mallaka.
Wallafawa ranar:
A cewar Sarakunan gargajiyar da suka fito daga kabilar Nama da Herero, euro biliyan daya bai isa diyyar kisan kare dangin da Jamusawan mulkin mallakar suka yi musu ba.
Matakin dai ya zo ne kwana guda bayan da a ranar Juma’a gwamnatin Jamus ta amince da aikata kisan kare dangi a Namibia a lokacin mulkin mallaka.
Turawan mulkin mallaka na Jamus sun kashe dubun dubatan kabilun ‘yan asalin Herero da Nama a wani kisan gillar da aka yi a shekarun 1904-1908 - wanda masana tarihi sukayi wa lakabi da kisan kare dangi na farko a karni na 20 da ya lalata dangantaka tsakanin Namibia da Jamus tsawon shekaru.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu