Isa ga babban shafi
Namibia

An bukaci Amurka ta shiga karkashin kotun ICC

Shugaban kasar Namibia, Hage Geingob, yace kasarsa zata ci gaba da zama cikin kotun hukunta manyan laifufuka ta ICC, muddin Amurka ta amince da halarcin kotun, yadda za’a dinga gurfanar da ‘yan kasarta a ciki.

Shugaban kasar Namibia Hage Geingob
Shugaban kasar Namibia Hage Geingob
Talla

Shugaban yace zargin da ake cewar kotun ICC, ta mayar da hankali ne kan kasashen Afirka gaskiya ne, saboda haka shigowar Amurka zai bada kwarin gwiwar ci gaba da zama a cikinta.

Geingob yace, lokaci yayi, da kasashen Afirka zasu bullo da wani tsari da ya dace da su ba tare da barin wasu kasashe suna yi musu katsalandan ba.

A watan Maris da ya gabata, gwamnatin Namibia ta ce zata janye daga karkashin kotun ICC saboda rashin adalci da gwamnatin ta ce kotun tana yi wajen gurfanar da wadanda ta ke zaba tare da kauda kai daga wadansu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.