Isa ga babban shafi
Habasha

Habasha ta sake tsaida lokacin zabukan da ta dage sau 2

Hukumar zaben Habasha ta bayyana ranar da zabukan kasar za su gudana, bayan dage gudanar zabukan da ta yi har sau 2 a baya.

Wasu mata 'yan kasar Habasha yayin shirin kada kuri'unsu a zabukan kasar na shekarar 2010.
Wasu mata 'yan kasar Habasha yayin shirin kada kuri'unsu a zabukan kasar na shekarar 2010. ASSOCIATED PRESS - Jerome Delay
Talla

Tun da fari dai, an tsara yin zabukan ne a watan Agustan shekarar bara, amma aka matsar da shi zuwa 5 ga watan Yuni na wannan shekara saboda barkewar annobar Korona.

Sai dai a makon jiya hukumar zaben Habasha ta sanar da sake dage zabukan saboda rashin isassun kayan aiki, wanda kuma jiya Juma’a ta bayyana 21 ga watan Yuni, a matsayin sabuwar ranar gudanar zabukan.

Zuwa karshen makon da ya gabata kididdiga ta nuna cewar ‘yan kasar Habasha kimanin miliyan 36 ne suka yi rijistar kada kuri’unsu a zabukan dake tafe, duk da rashin samun damar da wasu ‘yan kasar da dama suka yi, skamakon rikicin kabilancin day a addabi wasu sassan manyan yankunan kasar mafiya yawan jama’a da suka hada da Amhara da Oromia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.