Isa ga babban shafi
Habasha - Siyasa

Gwamnatin Habasha ta sake dage gudanar zabukan kasar

Hukumar zaben Habasha ta sanar da sake dage gudanar zabukan kasar, bayan da wasu jam’iyyun adawa suka kauracewa tsaida ‘yan takara da kuma yadda rikicin yankin Tigray ya tsananta ta yadda zabukan ba za su iya gudana ba a yankin.

Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed
Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed AP - Mulugeta Ayene
Talla

Hukumar zaben ta kuma bayyana fama da karancin kayaan aikin horas da jami’an ta da za su kula da zaben na ranar 5 ga watan Yuni da a yanzu aka dage shi zuwa wani lokacin da ba a fayyace ba.

Wasu 'yan gudun hijira da rikicin yankin Tigray ya raba da muhallansu yayin layin karbar abinci a wani sansani dake iyakar Habasha da Sudan.
Wasu 'yan gudun hijira da rikicin yankin Tigray ya raba da muhallansu yayin layin karbar abinci a wani sansani dake iyakar Habasha da Sudan. AP - Nariman El-Mofty

Tun da fari dai a watan Agustan shekarar bara ta 2020, aka tsara zabukan na Habasha za su gudana, amma aka dage saboda annobar Korona, sai dai a waccan lokacin, jam’iyyar TPLF dake mulkin yankin Tigray ta yi gaban kanta wajen gudanar da zabukan a watan Satumba, matakin da ya janyo fadan da ake gwabzawa tsakanin ‘yan tawayen yankin da sojojin Habasha tun daga watan Nuwamba zuwa wannan lokaci.

Kawo yanzu kuma rikicin na Tigray yayi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba wasu kusan dubu 100 da muhallansu, baya ga wasu dubban da suka tsere zuwa Jamhuriyar Congo da Sudan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.