Isa ga babban shafi
Zimbabwe-Coronavirus

Zimbabwe: Jami'an lafiya da dama sun ki karbar allurar rigakafin Korona

Ma’aikatan jinya a Zimbabwe sun ki yarda a yi musu allurar rigakafin Korona, sakamakon shakkun da suka ce suna shi kan ko za ta iya magance sabon nau’in cutar ta Korona da ta soma bulla a makwafciyarsu Afrika ta Kudu.

Wata ma'aikaciyar jinya a Zimbabwe yayin kokarin yiwa mataimakin shugaban kasar Constatino Chiwenga allurar rigakafin Korona, ranar 18 ga watan Fabarairu na 2021, lokacin da gwamnati ta kaddamar da shirin yiwa al'ummar kasar rigakafin annobar ta Korona.
Wata ma'aikaciyar jinya a Zimbabwe yayin kokarin yiwa mataimakin shugaban kasar Constatino Chiwenga allurar rigakafin Korona, ranar 18 ga watan Fabarairu na 2021, lokacin da gwamnati ta kaddamar da shirin yiwa al'ummar kasar rigakafin annobar ta Korona. AP - Tsvangirayi Mukwazhi
Talla

Shugaban kungiyar ma’aikatan jinya na kasar ta Zimbabwe Enock Dongo ne ya bayyana halin da ake ciki a karshen makon nan, inda yace mafi rinjayen 'ya'yan kungiyar da yawansu ya kai dubu 12, sun noke wajen yadda da maganin na Korona.

Ranar 18 ga watan Fabarairu gwamnatin Zimbabwe ta kaddamar da shirin yiwa al’ummarta allurar rigakafin cutar Korona, bayan sayen sunkin alluran Sinopharm dubu 200 da China ta samar, tare da alkawarin sayen karin wasu alluran kusan miliyan 2.

Binciken kwararru dai ya nuna cewar rigakafin na Sinopharm na da tasirin kashi 79 cikin 100 dakile cutar Korona.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.