Isa ga babban shafi
Somalia-MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a gaggauta gudanar da zabe a Somalia

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci bangarorin siyasar kasar Somalia da su cimma matsaya don gudanar da zaben shugaban kasa cikin gaggawa, bayan harbe harben da aka gani a karshen mako lokacin zanga zangar yan adawa a makon jiya.

Tawagar bangaren adawar Somalia yayin wani gangaminsu a birnin Mogadishu da nufin tirsasawa gwamnati gudanar da zaben kasar.
Tawagar bangaren adawar Somalia yayin wani gangaminsu a birnin Mogadishu da nufin tirsasawa gwamnati gudanar da zaben kasar. AFP
Talla

Jakadan Majalisar a Somalia James Swan ya shaidawa kwamitin sulhu cewar yana da muhimmanci shugabannin siyasar kasar da su daina daukar matakan tayar da hankali domin kaucewa jefa kasar a sabon rikici.

Kasar Somalia ta shirya gudanar da zaben shugaban kasa ranar 8 ga watan nan, amma kuma rashin gudanar da zaben ya haifar da rikici, inda 'yan adawa suka bukaci shugaban kasa Mohammed Abdullahi Farmajo ya sauka daga mukamin sa.

Somalia da ke fuskantar rikice-rikice baya ga hare-haren ta'addancin kungiyar al shebaab magoya bayan bangaren adawa na ci gaba da zanga-zangar adawa da gwamnati tare da kiran gudanar da zaben. 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.