Isa ga babban shafi
Somalia

An samu musayar wuta tsakanin 'yan adawa da jami'an tsaron Somalia

An samu musayar wuta a Mogadishu babban birnin Somalia da safiyar yau Juma’a lokacin da bangaren adawa ke wani gangami don nuna bacin ransu da matakin gaza gudanar da babban zaben kasar.

Somalia na ci gaba da fuskantar rikici siyasa da boren jama’a tun bayan da shugaba Mohamed Abdullahi Mohamed ya gaza gudanar da zaben kasar wanda bisa ka’ida yakamata a yi ranar 8 ga watan nan.
Somalia na ci gaba da fuskantar rikici siyasa da boren jama’a tun bayan da shugaba Mohamed Abdullahi Mohamed ya gaza gudanar da zaben kasar wanda bisa ka’ida yakamata a yi ranar 8 ga watan nan. Reuters
Talla

Tawagar bangaren adawar a gangamin na su na yau, sun ce basa daukar shugaba Muhammad da aka fi sani da Farmajo a matsayin shugaban kasar.

Rahotanni sun ce babu tabbaci kan bangaren da ya fara harbin a musayar wutar sai dai wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce da yiwuwar a samu tarin wadanda suka jikkata ko da babu asarar rayuka.

Gangamin bangaren adawar ya zo dai dai da shirin zanga-zangar da al’ummar kasar suka tsara gudanarwa wanda ay tilasta girke tarin jami’an tsaro a sassan birnin da kuma rufe manyan hanyoyi.

Somalia na ci gaba da fuskantar rikici siyasa da boren jama’a tun bayan da shugaba Mohamed Abdullahi Mohamed ya gaza gudanar da zaben kasar wanda bisa ka’ida yakamata a yi ranar 8 ga watan nan.

Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da kiraye-kirayen ganin an kwantar da hankula a kasar ta Afrika da ke fama da ta’addancin kungiyar Al Shebaab tsawon shekaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.