Isa ga babban shafi
Somalia

Al-Shebab ta kai hari wani Otel a Mogadishu

Akalla mutane uku suka mutu sakamakon harin da kungiyar Al Shebaab ta kai wani otel dake Mogadishu, bayan ta tada bam a cikin wata motar dake kofar shiga ginin.

Wani Otel da aka kaiwa hari a Somalia
Wani Otel da aka kaiwa hari a Somalia REUTERS/Feisal Omar
Talla

Rahotanni sun ce sojoji sun yiwa otel din da ake kira Hotel Afrik kawanya da kuma tare duk wani hanyar dake zuwa ginin dake hanyar tashar jiragen saman Mogadishu.

Wani jami’in Yan Sanda Mohammed Adan yace anyi musayar wuta tsakanin Yan bindigar da jami’an tsaro wadanda ke kokarin kubutar da jama’ar dake ginin.

Kungiyar Al-Shebaab ta dauki alhakin kai harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.