Isa ga babban shafi
Afrika

Harin ta'addanci a Somalia ya hallaka mutane 4

Wani harin kunar bakin wake da yan kungiyar Al Shebab suka kai Mogadiscio dake babban birnin kasar Somalia yayi sanadiyar mutuwar mutane hudu a jiya asabar.

Jami'a tsaron Somalia a harabar wani Otel da aka kai harin  kunar bakin wake
Jami'a tsaron Somalia a harabar wani Otel da aka kai harin kunar bakin wake REUTERS/Feisal Omar
Talla

Daga cikin mutanen da suka rasa rayukan su akwai yan kasar Turkiya biyu.

Biyo bayan wannan kazamin hari ,Turkiya ta bakin Ministan kiwon lafiyar kasar Fahrettin Koca,ta bayyana cewa wasu yan kasar uku sun samu munanan raunuka, wanda aka garzaya da su wani asibiti da Turkiyya ke kula da shi a Mogadiscio.

Ministan ya tabbatar da mutuwar yan turkiya biyu,da wasu jami’an tsaro dake tareda su a lokacin wannan hari.

Turkiya na daga cikin kasashen dake dafawa gwamnatin Somaliya tareda bayar da horo zuwa jami’an tsaron kasar dake fama da fadi tashi a yakin da suke da yan kungiyar Al Shebab.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.