Isa ga babban shafi
Cancer-Afrika

WHO ta sanar da samun karuwar sabbin kamuwa da Cancer a Afrika

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce masu fama da cutar kansa ko sankara a nahiyar Afirka sun karu inda yawan su ya ribanya a cikin shekaru 20 da suka gabata.

Wata Mata da ke jinyar Cancer a Uganda.
Wata Mata da ke jinyar Cancer a Uganda. RFI/Charlotte Cosset
Talla

Daraktan Hukumar da ke kula da nahiyar Afirka, Matshidiso Moeti ta ce adadin masu fama da cutar ya tashi daga dubu 338 a shekarar 2002 zuwa dubu 846, a shekarar 2020.

Jami’ar wadda ta aike da sakon bikin ranar yaki da cutar ta Duniya, ta ce a cikin shekaru 20 da suka gabata, sabbin masu kamuwa da cutar sun karu matuka, musamman ga masu fama da sankarar mama da na mahaifa da maraina da kuma koda.

Moeti ta danganta dalilan samun karuwar masu dauke da cutar da suka hada da tsufa da gado da busa sigari da shan barasa da abincin da ke dauke da suga da gishiri da maiko da rashin motsa jiki da kibar da ta wuce kima da kuma amfani da wasu sinadarai masu guba.

Alkaluma sun nuna cewar sabbin mutane dubu 124 da 815 aka tabbatar sun harbu da cutar a Najeriya a shekarar 2020, yayin da dubu 78 suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.