Isa ga babban shafi
Ghana

Majalisar Dokokin Ghana za ta koma zama sau 2 a mako saboda Covid-19

Majalisar dokokin kasar Ghana ta ce daga yanzu za ta dinga zama sau biyu ne kawai kowanne mako bayan da 'yan Majalisu 15 suka harbu da cutar korona, tare da wasu tarun ma’aikatan Majalisar.

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo.
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo. REUTERS/Francis Kokoroko
Talla

Shugaban Majalisar Alban Bagbin ya sanar da matakin, inda ya ce gwajin da aka yiwa 'yan Majalisun ya nuna cewar 15 daga cikin sun a dauke da cutar, kuma tuni aka basu shawarar killace kan su.

Bagbin ya kuma ce 56 daga cikin ma’aikatan Majalisar na dauke da cutar, abinda ya sa suka yanke hukuncin zama sau biyu kawai a mako, wato ranakun Talata da Alhamis domin kare lafiyar jama’a.

Shugaban kasa Nana Akufo-Addo ya sanar da daukar sabbin matakai a ranar lahadi wadanda suka hada da hana taruwar jama’a da kuma hana bukukuwa saboda karuwar masu harbuwa da cutar.

Kasar Ghana ta rufe iyakokin ta tun daga watan Maris na shekarar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.