Isa ga babban shafi
Ghana

Jam'iyyar NDC ta yi watsi da sakamakon zaben Ghana bayan nasarar Akufo-Addo

Babbar Jam’iyyar adawa a Ghana NDC ta yi watsi da sakamakon zaben kasar da ya nuna shugaba Nana Akufo-Addo a matsayin wanda ya lashe da gagarumin rinjaye.

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo da babban abokin karawarsa a zaben kasar John Mahama.
Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo da babban abokin karawarsa a zaben kasar John Mahama. venturesafrica
Talla

A ganawarsa da manema labarai, Haruna Iddrisu mamba a majalisar wakilan Ghanar karkashin jam’iyyar ta NDC ya ce suna da kwararan hujjojin da ke tabbatar musu babu shihanci a sakamakon da hukumar zaben kasar ta fitar.

Sakamakon zaben dai kamar yadda hukumar zaben Ghana ta wallafa ya nuna cewa Nana Akufo-Addo ya lashe kashi 51 da digo 59 na yawan kuri’un da aka kada yayinda babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar ta NDC John Mahama ya samu kashi 47 da digo 36.

Cikin jawabinsa a birnin Accra, Iddrisu ya bayyana cewa za su dauki dukkannin matakan da suka dace wajen kalubalantar ilahirin sakamakon zaben kama daga matakin shugaban kasa har zuwa ‘yan Majalisu.

Rundunar ‘yansandan Ghana dai ta sanar sa samun rahotanni tashe-tashen hankula har sau 60 a sassan kasar ranar zabe, ciki kuwa har da kisan mutum 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.