Isa ga babban shafi
Ghana

Nana Akufo-Addo ya sake lashe zaben Ghana

Hukumar zaben kasar Ghana ta sanar da shugaba Nana Akufo-Addo a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da akayi ranar litinin, bayan ya kada Yan takara 11 cikin su harda tsohon shugaban kasa John Dramani Mahama.

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo
Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo REUTERS/Francis Kokoroko
Talla

Shugabar hukumar zaben Jean Adukwei Mensa ta ce Akufo-Addo na Jam’iyyar NPP ya samu kuri’u miliyan 6 da dubu 730,413 wanda shine kasha 51.59 na kuri’un da aka kada, yayin da Mahama na NDC ya samu kuri’u miliyan 6 da dubu 214,889 wanda shine kashi 47.36.

Wannan ya nuna cewar shugaba Akufo-Addo ya samu nasarar zaben domin yin wa’adi na biyu.

Kafin gabatar da sakamakon magoya bayan Jam’iyyar adawa ta NDC sun yi kwarya kwaryar zanga zanga domin gabatar da korafin magudin zaben da suka ce dan takarar su ne ya samu nasara.

Rahotanni sun ce an gudanar zaben cikin kwanciyar hankali, sai dai Yan Sanda sun ce mutane 5 sun mutu sakamakon rikicin da ya barke bayan zaben.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.