Isa ga babban shafi

Al'ummar Ghana na kada kuri'a a zaben shugaban kasa

Yau al'ummar kasar Ghana ke gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan Majalisu, inda 'yan takara 12 cikin su har da mata  3 ke fafatawa.

Wasu daga cikin 'yan takaran shugabancin Ghana, har da shugaba mai ci, Nana Akufo Addo sun sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya.
Wasu daga cikin 'yan takaran shugabancin Ghana, har da shugaba mai ci, Nana Akufo Addo sun sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya. RFI
Talla

Wannan shine karo na 3 da shugaba Nana Akufo-Addo da tsohon shugaban kasa John Dramani Mahama ke fafatawa a tsakanin su.

A karawar da suka yi sau biyu, Mahama ya samu nasara sau guda a shekarar 2012, yayin da Akufo-Addo ya kada shi a shekarar 2016.

Matsalar tattalin arziki da tsaro da rashin ayyukan yi ga matasa da kuma annobar korona na daga cikin manyan batutuwan da suka mamaye yakin neman zaben.

Rahotanni daga hukumar zabe sun ce mutane miliyan 17 suka yi rajistar kada kuri’a a wannan zaben, sai dai sau tari a kasashen Afirka, mutane ba su cika fitowa żabę sosai ba.

Barazanar tashin hankalı da kuma cutar korona na daga cikin abin da ke yi wa wannan zabe barazana, amma shugaban kasa Akufo-Addo ya sha alwashin samar da tsaro ga masu kada kuri’a domin ganin sun sauke nauyin dake kań su, a jawabin da ya y iwa al’ummar Ghana daren  Lahadi.

Shugabar hukumar zabe Jean Mensah ta sha alwashin ganin an samu karbabben zaben da duniya zata amince da shi, yayın da tayi watsi da zargin Jam’iyyar adawa ta NDC cewar ta hana 'yan kasar, masu dauke da fasfo na wasu kasashe damar shiga zaben, musamman 'yan Ghana da suka fito daga Togo.

Ana saran karin mutane miliyan biyu zasu shiga zaben sabanin na shekarar 2016, yayin da Hukumar zaben ta sha alwashin bayyana sakamakonsa da wuri.

Tuni masu sa ido daga kasashen ECOWAS da kungiyar kasashen Afirka ta AU da Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar kasashen Turai suka isa Ghana domin sanya ido kań yadda zaben zai gudana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.