Isa ga babban shafi
Afrika

An kammala yakin neman zaben kasar Ghana

A jiya asabar aka kammala yakin neman zaben Shugabancin kasar Ghana da zai gudana a gobe Litinin, yakin neman zaben da ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana bayan da 'yan takara a zaben kasar suka sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya a karkashin inuwar hukumar zaman lafiya ta Ghana.

'Yan takaran shugabancin Ghana sun sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya.
'Yan takaran shugabancin Ghana sun sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya. RFI
Talla

Yan takara 12 ne za su fafata wajen neman kujerar shugaban kasa, daga cikin su har da Shugaba mai ci Nana Akoufo Ado.

Bayanai na nuna cewa akalla mutane milyan 17 ne hukumar zaben kasar ta bayyana cewa sun karbi katunan zabensu.

Rahotanni daga kasar na nuni da cewa wakilai 'yan sa ido a zaben sun soma isa kasar, yayinda kungiyar kasashen Afrika ta yi kira ga 'yan siyasa na ganin kowanen su ya amince da sakamakon zaben, wanda yin hakan zai tabbatar da matsayin kasar a idanun Duniya na cewa Ghana na daga cikin kasashen Afrika da demokradiyya ta samun kujerar zama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.