Isa ga babban shafi
Ghana

Zaben Ghana: 'Yan takara sun sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya

'Yan takaran shugaban kasar Ghana 12 yau sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya domin ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali ba tare da samun tashin hankali ba.

'Yan takaran shugabancin Ghana sun sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya.
'Yan takaran shugabancin Ghana sun sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya. RFI
Talla

Daga cikin 'yan takaran akwai shugaban kasa Nana Akufo-Addo da babban abokin hamayar sa kuma tsohon shugaban kasa John Dramani Mahama wadanda a karo na 3 suke fafatawa a tsakanin su.

Masu rajistar zabe sama da miliyan 17 ake saran zasu kada kuri’a a zaben da zai gudana ranar Litinin wanda shine na 8 a jere da ake samu a cikin kasar wadda ta kwashe shekaru 30 tana tafiyar da dimokiradiya ba tare da samun targade ba.

Masu sanya ido na hasashen samun nasarar shugaban, yayin da Jam’iyyar adawa ta NPP kuma ta cigaba da rike rinjayen da take da shi a Majalisar dokoki mai kujeru 275.

A shekarar 2012 Mahama ya kada Akufo-Addo lokacin da ya samu sama da kashi 50 da rabi na kuri’un da aka kada, yayin da a shekarar 2016 Akufo-Addo ya kada Mahama da kashi 53 da rabi.

Ana kallon Ghana a matsayin daya daga cikin kasashen da mulkin dimokiradiya ya dore a cikin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.