Isa ga babban shafi
Ghana

Tsohon shugaban Ghana J.J Rawlings ya rasu

Tsohon shugaban Ghana, Jerry John Rawlings ya rasu a safiyar Alhamis din nan a birnin Accra bayan ya yi fama da rashin lafiya kamar yadda jaridun kasar suka rawaito.

Marigayi tsohon shugaban Ghana John Jerry Rawlings
Marigayi tsohon shugaban Ghana John Jerry Rawlings © Pruneau/Wikimedia Commons
Talla

J.J Rawlings da aka haifa a ranar 22 ga watan Yunin 1947, ya kwashe tsawon mako guda yana jinya a Asibitin Koyarwa na Korle Bu gabanin rasuwarsa.

Jaridar Graphics ta ce, Rawlings ya kwanta rashin lafiya ne tun bayan da aka gudanar da jana’izar mahaifiyarsa makwanni uku da suka gabata.

Mista Rawlings ya jagoranci mulkin sojin Ghana daga shekarar 1981 zuwa 1992 kafin daga bisani ya sake yin wa’adi har sau biyu a matsayin shugaban da aka zaba kan turbar demokuradiya daga watan Janairun 1993 zuwa watan Janairun shekarar 2001.

Marigayin ya fara jagoantar kasar ne a matsayin jami’in sojin sama bayan juyin mulkin da aka yi a shekarar 1979.

Gabanin nasararsa ta darewa kan karagar mulkin kasar, Rawlings ya taba jaorantar juyin mulkin da bai yi nasara ba a ranar 15 ga watan Mayun shekarar 1979.

Rawlings ya mika mulki ga farar hula, amma daga bisani ya sake karbe ragamar kasar a ranar 31 ga watan Disamban shekarar 1981.

A shekarar 1992 ne, Rawlings ya yi murabus daga aikin soji, inda ya kafa jam’iyyar NDC wadda a karkashin inuwarta ya sake zama shugaban kasa a Jamhuriya ta hudu.

Kazalika an sake zaben sa a shekarar 1996 domin yin karin wa’adin shekaru hudu.

Ya rasu ya bar ‘ya’ya hudu da matarsa guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.