Isa ga babban shafi
Ghana-Zabe

Manyan jam'iyyu sun yi ikirarin lashe zaben Ghana

Jagoran ‘yan adawan Ghana John Mahama ya gargadi shugaba mai ci Nana Akufo-Addo game da yunkurin tafka magudin zabe a daidai lokacin da bangarorin biyu ke ikirarin samun nasara duk da cewa, ba a fitar da sakamakon karshe a hukumance ba.

John Mahama tare da Nana Akufo-Addo
John Mahama tare da Nana Akufo-Addo venturesafrica
Talla

Kalaman Mahama sun haddasa tayar da jijiyoyin wuya a Ghana, kasar da aka yi wa kyakkyawar shedar gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.

Mahama ya shaida wa taron manema labarai cewa, ba su amince da abubuwan da ke wakana ba kuma Nana Akufo-Addo na ci gaba da gabatar da ikirarin da ya saba wa demokuradiya.

Madugun 'yan adawan mai shekaru 62 ya kara da cewa, bai dace shugaba Akufo-Addo ya yi amfani da sojoji ba wajen sauya sakamakon zaben a wasu mazabu da ya ce jam’iyyarsa ce ta lashe, yana mai jaddada cewa, ba za su lamunci haka ba.

Kodayake Ministan Yada Labarai na Ghana, Kojo Oppong Nkrumah ya musanta zargin amfani da sojoji da zummar tafka magudi a zaben na shugaban kasa da na ‘yan majalisa.

Fadar shugaban kasa ta fitar da nata sakamakon da ta tattara, inda ta ce, shugaba mai ci na da kashi 52.25, yayin da Mahama ke da kashi 46.44.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.