Isa ga babban shafi
Afrika

John Mahama na neman kotun Ghana ta soke zaben kasar

Tsohon shugaban Ghana kuma dan takarar da ya zo na biyu a zaben shugabancin kasar da ya gudana a watan Disambar da ya kare John Mahama, ya shigar da kara kotun Koli, inda yake kalubalantar nasarar sake zarcewa da shugaba mai ci Nana Akufo Addo ya samu.

John Dramani Mahama tsohon Shugaban kasar Ghana tareda Nana Akoufo Addo da ya lashe zaben kasar Ghana
John Dramani Mahama tsohon Shugaban kasar Ghana tareda Nana Akoufo Addo da ya lashe zaben kasar Ghana venturesafrica
Talla

Ranar 9 ga watan Disamba ne hukumar zaben kasar ta Ghana ta sanar da shugaba Nana Akufo-Addo a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar, bayan ya kada Yan takara 11 cikin su harda tsohon shugaban kasa John Dramani Mahama.

Shugabar hukumar zaben Jean Adukwei Mensa ta ce Akufo-Addo na Jam’iyyar NPP ya samu kuri’u miliyan 6 da dubu 730,413 wanda shine kasha 51.59 na kuri’un da aka kada, yayin da Mahama na NDC ya samu kuri’u miliyan 6 da dubu 214,889 wanda shine kashi 47.36.

Wannan ya nuna cewar shugaba Akufo-Addo ya samu nasarar zaben domin yin wa’adi na biyu.

Kafin gabatar da sakamakon magoya bayan Jam’iyyar adawa ta NDC sun yi kwarya kwaryar zanga zanga domin gabatar da korafin magudin zaben da suka ce dan takarar su ne ya samu nasara.

John Mahama na neman kotun da ta soke zaben da ya ce an murde sakamakonsa tare da bada umarnin shirya sabo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.