Isa ga babban shafi
Ghana

Anyi jana'izar tsohon shugaban kasar Ghana Jerry John Rawlings

Laraban nan aka kammala jana’izar tsohon shugaban kasar Ghana Jerry John Rawlings wanda ya rasu ranar 12 ga watan Nuwambar bara yana da shekaru 73 a duniya.

Tsohon shugaban kasar Ghana Jerry Rawlings.
Tsohon shugaban kasar Ghana Jerry Rawlings. REUTERS
Talla

An yi ta wake-waken karramawar bangirma a dandalın ‘yancin Accra, inda aka gudanar da jana’izar tsohon shugaban kasa Jerry Rawlings wanda ya samu halartar mutane da dama.

Shugaban kasa Nana Akufo-Addo ya jinjinawa tsohon shugaban saboda rawar da ya taka lokacin da ya siga faren siyasar Ghana.

Shugaba Addo yace wannan ya sa mutanen Ghana ke ganin kimar tsohon shugaban

JJ Rawlings ya zama shugaban kasar Ghana ne a shekarar 1979, inda ya mika mulki kafin daga bisani ya dawo karara a ranar 31 ga watan Disambar shekarar 1981, abinda ya bashi damar kwashe shekaru 11 a karagar mulki, ya kuma zama shugaban kasar da yafi dadewa a karalar a tarihin Ghana.

Nana Akufo Addo

"Juyin mulkin da ya kawar da Janar Kotou Archampong daga karagar mulki da kuma kawo Janar Fred Akuffour a madadin sa ya gabatar da Fl Lt Jerry John Rawlings a fagen siyasar kasar mu. Shugaba ne mai dauke hankalin jama’a, mai karsashi, mara tsoro".

"Wannan shine kirarin da mutanen Ghana ke yiwa Jerry John Rawlings, matashin sojin sama, wanda ya gabatar da kan sa a fagen siyasar Ghana wajen yunkurin juyin mulkin shekarar 1979, aka kuma yanke masa hukuncin kisa saboda yunkurin. A lokacin da ake masa shari’a ya gabatar da irin halayen sa, lokacin da ya tashi a gaban kotun soji, ya dauki alhakin juyin mulkin, ya kuma bukaci sakin sojojin dake tare da shi".

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.