Isa ga babban shafi
Afrika

An rantsar da Nana Akufo Addo a Accra

Shugaban Ghana Nana Akufo Addo ya yi rantsuwar kama aiki a wa’adin shugabancin kasar karo na biyu, bayan samun nasarar zarcewar da yayi a zaben da ya gudana a farkon Disambar shekarar 2020 da ya gabata.

Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo.
Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo. REUTERS/Francis Kokoroko
Talla

Shugabanin kasashen yammacin Afrika da suka halarci bikin rantsar da Nana Akufo Addo sun hada da Alassane Ouattara,Faure Gnassingbe,Mahamadou Issoufou da wasu manyan baki daga ciki da wajen kasar.

Kafin bikin rantsuwar rikici ya barke a zauren majalisar dokokin kasar, inda aka rika baiwa hammata Iska a tsakanin abokan hamayya, kan zaben kakakin majalisar, lamarin da yasa sai da sojoji suka shiga tsakani. 'Yan Majalisun sun zabi Alban Bagbin daga jam'iyyar adawa ta NDC ,wanda ya samu kuri'u 138 yayinda masu mulki suka tashi da kuri'u 136.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.