Isa ga babban shafi
Afrika

Dan takara Bazoum Mohammed na kan gaba a zaben Nijar

A Jamhuriyar Nijar alkaluma daga hukumar zaben kasar na nuni cewa tsohon ministan cikin gida kuma dan takarar jam’iyya mai mulki Bazoum Mohammed na PNDS ke kan gaba a zaben shugaban kasa zagaye na farko da ya gudana ranar 27 ga watan Disamba na shekara ta 2020 a gaban abokin takarar sa  tsohon Shugaban kasar Mahamane Ousmane.

Bazoum Mohammed da abokin takarar sa Mahamane Ousmane
Bazoum Mohammed da abokin takarar sa Mahamane Ousmane RFI Hausa
Talla

Akaluman da hukumar zaben Nijar ta tattara daga yankuna 266 daga cikin 266 dai sun nuna yawan kuri’un da Bazoum Mohammed ya samu sun kai  1.879.000, yayin da mai bi masa Mahamane Ousmane na jam’iyyar adawa ta RDR Canji ke da kuri'u 811.000.

Ranar 21 ga watan fabrairu 2021 ne za a gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu da zai hada Bazoum Mohammed na PNDS da Mahaman Ousmane daga jam'iyyar RDR Canji.

Yan takara Seyni Oumarou na MNSD ya samu kashi 8,95% na kuri'u,Albade Abouba na Jamhuriya MPR ya samu kashi 7,07% sai Ibrahim Yakouba  na jam'iyyar MPN Kishin kasa da ya samu kashi 5,38%,tsohon Shugaban mulkin sojin kasar Salou Djibo na jam'iyyar PJP generation Dubara ya tashi da kashi 2,99% na kuri'u.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.