Isa ga babban shafi
Afrika

An kammala yakin neman zaben kasar Nijar

Akala mutane milyan 7 da dubu 400 ne ake sa ran za su kada kuri’ar su a zaben Shugaban kasa da na yan Majalisu da zai gudana a gobe lahadi a Jamhuriyar Nijar. Zaben da zai zama irinsa na farko da za a mika mulki daga farar hula zuwa farar hula bisa turbar demokradiyya a tarihin kasar, duk da barazanar tattalin arziki da kuma hare-haren mayakan jihadi da yan Boko haram.

Wasu daga cikin matan da suka karbi katunan zabe a Jamhuriyar Nijar
Wasu daga cikin matan da suka karbi katunan zabe a Jamhuriyar Nijar Issouf Sanogo/AFP/Getty Images
Talla

A cikin makon da ya gabata ne 'yan takara 7 daga cikin 30 dake neman maye gurbin shugaban kasa Issofou Mahammadou suka shigar da kara kotu inda suke bukatar ganin ta haramtawa Bazoum takara, amma kuma kotun tayi watsi da bukatar su.

Daga cikin wadannan yan takara akwai tsohon shugaban mulkin soji Janar Salou Djibo da Amadou Boubacar Cisse da Ibrahim Yacouba da Omar Hamidou Tchiana.

Sauran sun hada da Hamissou Mahaman Moumouni da Mamadou Moustapha Mamadou da Aboulkadri Alpha Oumarou da kuma Djibrilla Bare.

Dan takara bangaren gwamnmati Bazoum Mohammed a wata zantawa da kamfanin dillancin labaren Faransa na Afp ya dau alkawalin dawo da ilahirin yan gudun hijira na gabcin kasar gidajen su nan da karshen shekara ta 2021.

A bangaren yan adawa, dawo da tsaro,bunkasa ayukan noma na daga cikin manyan ayuka da suke sa ran dawo da su a wasu yankunan da rashin tsaro ya tilastawa mazauna yankunan kauracewa gidajen su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.