Isa ga babban shafi
Habasha

Dakarun Habasha sun halaka maharan da suka yi kisan kiyashi a Bekoji

Rundunar sojin Habasha ta girke dakarunta a Benishangul-Gumuz dake yammacin kasar, kwana guda bayan da ‘yan bindiga suka kashe sama da mutane 100 a yankin mai fama da rikicin kabilanci.

Sojojin kasar Habasha
Sojojin kasar Habasha Reuters
Talla

A Larabar da ta gabata 23 ga watan Disamba, da sanyin safiya gungun mahara suka afkawa kauyen Bekoji dake garin Metekel da ya kunshi kabilu daban daban, inda suka kashe sama da mutane 100, kisan gillar da hukumar kare hakkin dan adam ta Habasha ta tabbatar aukuwarsa.

Sai dai rahotanni sun ce daga bisani sojojin kasar ta Habasha sun samu nasarar halaka 42 daga cikin ‘yan bindigar da suka aikata kisan gillar a kauyen na Bekoji.

A gefe guda gwamnatin Habasha na cigaba da gwabza yaki da ‘yan tawayen TPLF a yankin Tigray dake arewacin kasar tsawon makwanni 6, fadan da ya raba kusan mutane dubu 950 da muhallansu.

Habasha dake matsayin kasa ta biyu mafi yawan al’umma a Afrika na fuskantar rikice-rikice ne tun bayan da Fira Minista Abiy Ahmed ya karbi jagorancin kasar a 2018, wanda ya soma daukar matakan garambawul ga tsarin tattalin arzikin kasar da kuma Dimokaradiyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.