Isa ga babban shafi
Habasha

'Yan bindiga sun kashe fararen hula 100 a Habasha

Hukumar kare hakkin dan Adam ta Habasha ta sanar da yadda ‘yan bindiga suka hallaka mutane fiye da 100 a wani farmakin baya-bayan nan da suka kai kan fararen hula a yankin Benishangul-Gumuz.

Firaministan Habasha Abiy Ahmed.
Firaministan Habasha Abiy Ahmed. REUTERS/Kumera Gemechu
Talla

Cikin sanarwar da hukumar ta fitar ta ce ‘yan bindigar sun farmaki gundumar Metekel inda suka rika barin wuta baya ga kone gidaje tun da safiyar jiya laraba har zuwa yammaci ba tare da al’ummar yankin sun samu dauki daga jami’an tsaro ba.

Hukumar ta ce tana da cikakkun hujjoji da kuma hotunan yadda al’amarin ya faru.

Hukumar ta ce akwai mutane 36 da suka jikkata a farmakin ciki har da wadanda aka cirewa tarin alburusai inda yanzu haka suke ci gaba da karbar kulawa a asibiti.

Babban kalubalen da ya dabaibaye gwamnatin shugaba Abiy Ahmed bai wuce rikicin kabilanci da ke ci gaba da tsananta a sassan kasar ta Habasha ba.

Hukumar kare hakkin dan adam din ta ce yanzu haka an kame wasu mutane 5 da ke da hannu a farmkin inda su ke fuskantar tuhuma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.