kasashen Sudan da Habasha sun fara tattaunawa don shawo kan rikicin dake tsakanin su
Gwamnatocin kasashen Sudan da Habasha sun fara tattaunawa don shawo kan rikicin da bangarorin biyu suka fuskanta cikin makon jiya game da kan iyakarsu.
Wallafawa ranar:
Wasu rahotanni sun bayyana yadda dakarun Habasha suka farwa Sojin Sudan da ke tsaron kan iyaka tare da kashe 4 baya ga jikkata wasu 20 a makon jiya.
A watan da ya gabata ,Majalaisar Dinkin Duniya tace Sudan na bukatar akalla dala miliyan 150 domin taimakawa yan gudun hijirar da suka fito daga Habasha sakamakon tashin hankalin dake gudana a Yankin Tigray.
Shugaban hukumar kula da Yan gudun hijira na Majalisar Filippo Grandi ya bayyana haka bayan ya ziyarci inda aka tsugunar da Yan gudun hijira akalla 43,000 da suka samu mafaka a cikin kasar.
Tuni dai mataimakin Firaministan Habasha Demeke Mekonnen ya isa birnin Khartoum don tattaunawa kan rikicin tare da bayar da hakuri.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu