Isa ga babban shafi
Afrika

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta zargi Bozize da yunkurin juyin mulki

Gwamnatin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ta zargi tsohon shugaban kasa Francois Bozize da yunkurin juyin mulki, yayin da kungiyoyin Yan Tawayen kasar guda 3 suka sanar da kafa kawance a tsakanın su a daidai lokacin da ake sihrin gudanar da zaben shugaban kasa a makon gobe

François Bozizé, tsohon shugaban Afrika ta Tsakiya
François Bozizé, tsohon shugaban Afrika ta Tsakiya REUTERS/Luc Gnago
Talla

Sanarwar hadin gwuiwar kungiyoyin Yan tawayen zai dada jefa fargaba ganin yadda ake cigaba da zaman dar-dar a kasar dake fama da tashin hankali, yayin da Yan adawa ke zargin cewar gwamnati na shirin yin magudi a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun da za’ayi ranar 27 ga watan nan.

Kungiyoyin Yan tawayen sun gabatar da sanarwar hadin gwuiwa wadda ke bayyana shirin hadewar su wuri guda da za’a dinga kiran su ‘Coalition for Change’ a karkashin shugabanci guda.

Kungiyoyin sun bukaci daukacin magoya bayan su da su mutunta fararen hula da kuma karę muradun su, tare da bukatar ganin sun baiwa motocin Majalisar Dinkin Duniya da na kungiyoyin agaji damar gudanar da aikin su.

Sai dai gwamnatin kasar ta yi zargin cewar yanzu haka tsohon shugaban kasa Francois Bozize na garin Bossembele dake da nisan kilomita 150 daga Bangui inda yake shirya magoya bayan sa domin tattaki zuwa baban binin kasar.

Kakakin gwamnati Ange-Maxime Kaagui ya bayyana matakin a matsayin yunkurin kifar da gwamnati, bayan ya zargi magoya bayan tsohon shugaban da kashe jami’an Jandarmeri guda 3 da soja guda.

Hukumar zaben kasar ta haramtawa Bozize shiga takarar zaben da za’ayi makon gobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.