Isa ga babban shafi
Afrika

Ganawar sulhu tsakanin Bozize da Djotodiya a Bangui

Tsofin shugabanin kasashen Afrika ta tsakiya ,Francois Bozize da Michel Djotodiya sun samu ganawa a jiya juma’a a babban birnin kasar Bangui.Kusan mako daya kenan da Michel Djotodiya musulmi na farko da ya shugabanci kasar ya dawo gida bayan da ya share kusan shekaru shida ya na gudun hijira.

Tsofin Shugabanin kasar Afrika ta Tsakiya  Michel Djotodia da François Bozizé
Tsofin Shugabanin kasar Afrika ta Tsakiya Michel Djotodia da François Bozizé AFP/Simon Maina
Talla

Ganawar da suka share kusan rabin awa suna yi na zuwa ne a wani lokacin da ake radin-radin cewa za a dage zaben shugabancin kasar da za a yi ranar 27 ga watan Disemban shekar bana.

Francois Bozize tsohon shugaban kasar ya sanar da takarar sa a zaben dake tahe,Bozize na daga cikin yan takara da ake hasashen zai iya kawo cikas  ga sake zaben shugaban kasa mai ci Faustin Archange Touadera.

Yan lokuta da kamala wana tattaunawa tsakanin tsofin Shugabanin kasar,Michel Djotodiya ya sheidawa manema labarai cewa ya nemi ya gana da tsohon Shugaban kasar ne don su duba hanyoyin tabbatar da dawamamiyar zaman lafiya a kasar da aka share wani lokaci ana fama da fadan kabilanci.

Kotun fasalta kundin tsarin mulkin kasar ta gabatar da wannan hukumci ne, bayan da alkalan kotun suka sanar da soke takarar wasu karin yan takara 3 a zaben da zai gudana ranar 27 ga watan nan.

A watan Satumba na shekarar 2020 ne tsofin shugabanin kasashen Afrika ta tsakiya, Francois Bozize da Michel Djotodiya suka samu ganawa a babban birnin kasar Bangui.

Tsohon Shugaban kasar Michel Djotodiya musulmi na farko da ya shugabanci kasar ya dawo gida bayan da ya share kusan shekaru shida ya na gudun hijira a Jamhuriyar Benin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.