Isa ga babban shafi
Afrika ta tsakiya

Bozize zai shiga takara a zaben Afrika ta tsakiya

Hambararren Shugaban kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya Francois Bozize zai koma gida daga inda ya samu mafaka don tsayawa takarar zaben shugaban kasa da za a yi a watan Oktoba, kamar yadda Jam’iyyarsa ta sanar.

Tsohon Shugaban Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya François Bozizé
Tsohon Shugaban Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya François Bozizé AFP/Sia Kambou
Talla

Ana ganin komawarsa gida na iya haifar da rudani ganin gwamnatin da ta gaje shi ta aika da sammacin kama shi ga ‘Yan Sandan duniya a shekarar 2013, inda ake zarginsa da aikata laifukan yaki.

Majalisar Dinkin Duniya kuma ta kakaba ma shi takunkumin tafiye-tafiye.

Sakataren Jam’iyyarsa Bertin Bea ya ce Bozize zai dawo domin fara yakin neman zaben shugaban kasa.

Bozize ya tsere zuwa Kamaru, amma yanzu yana rayuwa a kasashen Uganda da Kenya.

Bayan Faduwar gwamnatin Bozize ne dai rikici ya barke tsakanin Mayakan Anti-balaka kiristoci da Seleka mafi yawancinsu musulmi wadanda suka hambarar da gwamnatinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.