Isa ga babban shafi
Afrika ta tsakiya

Ana tilastawa Musulmi yin ridda a Afrika ta tsakiya

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International tace ana tilastawa musulmi yin ridda a Kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiyar muddin suna son zama a kasar.

Kiristocin Mayakan kungiyar anti-balaka a Afrika ta tsakiya
Kiristocin Mayakan kungiyar anti-balaka a Afrika ta tsakiya AFP / Andoni Lubaki
Talla

Joanne Marines wata jami’ar Kungiyar mai cibiya a London ta fadi cewa mayakan kungiyar Anti-Balaka da suka tilastawa dubban musulmi barin kasar, a bara, yanzu sukan gindaya sharudda ne ga musulmi da ke komawa kasar, cewa muddin suna son zama to kada suyi addininsu.

Rayukan dubban mutane aka rasa, wasu dubban suka rasa muhalli sakamakon rikici tsakanin musulmi da ake kira mayakan Seleka da kuma kiristoci da ake kira mayakan anti-Balaka.

Rahoton kungiyar ta Amnesty na cewa da yawa mayaka na kungiyar kiristoci na anti-Balaka na barazanar kashe duk wani musulmi da aka ga yana yin ibadarsa, kuma akwai alamu da yawa musulmin da ke komawa kasar ta Jamhuriyar Tsakiyar Afrika an tursasa ma su yin ridda.

Saboda haka ne kungiyar ta Amnesty ta roki Gwamnatin kasar da Majalisar Dinkin Duniya da manyan kasashen da su sa baki domin gudun kazancewar lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.