Isa ga babban shafi
Afrika ta tsakiya

An sallami yara 350 daga aikin soja a Afirka ta Tsakiya

A Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya yara kanana 350 ne aka sanar da cewa kungiyoyin ‘yan tawayen kasar sun sallama bayan sun share shekaru suna aikin soja.

wasu makamai da aka kwace daga 'yan tawaye
wasu makamai da aka kwace daga 'yan tawaye AFP PHOTO / PACOME PABANDJI
Talla

Rahotanni sun ce wadannan yara ne da shekarunsu ba su kai 12 ba a duniya, kuma daukarsu aiki na a matsayin abin da ya saba wa doka.

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dai kasa ce da ta share tsawon shekaru biyu tana fama da yakin basasa, lamarin da ya bai wa kungiyoyin ‘yan tawaye damar daukar yara kanana domin sanya su aikin soja.

Manzon Asusu Kanana Yara na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mohamed Malick Fall, ya ce sallamar yaran daga aikin soja wata alama ce da ke nuna cewa ana kan hanyar samun zaman lafiya a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.